FALALAR KARANTA SURATUL- KAHFI A RANAR JUMU'AH Annabi (Saww) Yace : ''Duk ! wanda ya karanta Suratul-kahfi a Ranar jumu'ah, Zata kasance haske a gareshi wanda zai Haskake shi har zuwa wata Jumu'ah mai zuwa.'' DUBA A CIKIN : ( MUSTADRAK NA IMAM HAKIM JUZU'I NA 2, SHAFI NA 399.) ''AL-BAYHAQI 3/249. ''FAYDUL-QADEERJUZU'I NA 6, SHAFI NA 198.'' SHAYKH ALBANIY YA INGANTA SHI A CIKIN : SAHIHUL JAAMI' HADISI NA 6470.'' a wani hadisi kuma : An kar6o daga Dan Umar (R.A) yace Manzon Allah tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi yace : ''WANDA DUK ! YA KARANTA SURATUL- KAHFI A RANAR JUMU'AH HASKE ZAI KASANCE A GARESHI DAGA KASAN DUGA-DUGAN SA, HAR ! ZUWA GIRA-GIZAI DAKE A SAMA, KUMA ZATA KASANCE HASKE A GARESHI RANAR QIYAMA, KUMA ZA'A YAFE MASA (ZUNUBBANSA) DAKE TSAKANIN JUMU'AH GUDA BIYU.'' DUBA A CIKIN : (Al-Targheeb Wal-Tarheeb, juzu'i na 1, shafi na 298.) Kuma kada mu manta da Yawaita salati ga Annabi (Saww) a wannan Ranar. Happy jum,ah mubaraka daga farfajiyar alkhairi Allah ka Amsa mana ibadunmu