SALLAR BIYAN BUKATA NAN TAKE A DAREN JUMA'A A daren Juma'a, ka yi wanka. Ka sa tufa mai tsarki da tsafta kuma mai kyau, Ka yi sallah raka'a hudu da sallama biyu. Ka karanta a raka'ar farko Fatiha, sai : ﺍﻓﻮﺽ ﺍﻣﺮﻱ ﺍﻟﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺑﺼﻴﺮ ﺑﺎﻟﻌﺒﺎﺩ "Ufawwidu amri ilallah. Innallaha basirun bil ibad" sau dari (100). A raka'a ta biyu ka karanta Fatiha, sai : ﻧﺼﺮ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻭ ﻓﺘﺢ ﻗﺮﻳﺐ "Nasrun minallahi wa fatahun qarib" sau 100. A raka'a ta uku ka karanta Fatiha, sai : ﺍﻻ ﺍﻟﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﺗﺼﻴﺮ ﺍﻻﻣﻮﺭ "Ala ilallahi tasirul umur" sau 100. A raka'a ta hudu ka karanta Fatiha, sai : ﺍﻧﺎ ﻓﺘﺤﻨﺎ ﻟﻚ ﻓﺘﺤﺎ ﻣﺒﻴﻨﺎ "Inna fatahna laka fat-han mubinah" sau 100. Bayan sallama sai ka fada sau 100 ﻏﻔﺮﺍﻧﻚ ﺭﺑﻨﺎ ﻭﺍﻟﻴﻚ ﺍﻟﻤﺼﻴﺮ "Gufranaka Rabbana wa ilaikal masir" Sannan sai ka yi sujuda ka ce sau 100 ﺍﺳﺘﻐﻔﺮ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﺗﻮﺏ ﺍﻟﻴﻪ "Astagfirullah wa atubu ilaih" Za ka samu biyan bukata nan take da izinin Allah. Daren Juma'a shi ne ranar Alhamis da daddare. In kuma ya kubuce maka to kana iya yi Jumaa da da