KADA KASAKE HARAMUN TAZAMTO ITACE ABINCINKA
An karbo daga Abi Hurairata,(Allah yayarda dashi)yace "manzon Allah tsira da amincin Allah sutabbata agatrshi yace,"Allah madaukakin sarki tsarkakakkene,kuma baya karbar Abu sai me tsarki,kuma kuma hakika Allah ya umarci muminai da abinda ya Umarci Ma'aika sai Allah Madaukakin sarki ya ce,"yaku Manzanni,kuci daga halal,kuma kuyi Aiki nagari".kuma madaukakin Sarki yace "yaku wadanda kuka bada gaskiya,kuci daga tsarkakakkun abinda muka azurtaku,da'annan Annabi Alaihissalam ya ambaci wani mutum wanda dayake tsawaita tafiya,mai suma duguzum! mai kura yana mika hannunsa sama yana cewa,"ya Ubangiji ya Ubangiji".Gashi kuwa abincinsa na haram ne,kuma abin shansa na haram ne,kuma tufarsa haramce,kuma da haram aka ciyar dashi yana Yaro,to tayaya za'a amsa masa!!!?.Musulimne ya Ruwaito.
kunga wannan hadisin atakaice yana nuna mana illar cin Haramun ko shan haramun kokuma xiyarda iyali da Haramun.Amma abin kaico wannan zamani namu muna kewaye da haramun tako ina.kai takaima har Haramun din binta muke aguje amma saimun 'kwamusota mun tura Aljihunanmu.
ya Allah muna kamun kafa da Alfarmar Shugaba ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ka azurtamu da hakurin Neman halal komai dacinta da wuyarta Allah kada kasa mumutu dajikkunanmu Wanda yaginu da Haram kabamu ikon mutuwa da jikin da aka Gina da Halal.domin Annabi sAww yace duk jikin da aka gina da haram to bazai shiga Aljannaba.
Allah ka kiyayemu Ameeen summa Ameeen
Post a Comment
Post a Comment