KU NATSU KU KARANTA FALALAR SALATIN ANNABI ﷺ A DAREN JUMA'A DAKUMA YININ JUMA'A, KU TURAWA MASOYA ANNABI Sallallahu Alaihi wasallam #DAN_ANNABI_kuyi_SHERE_wanna_karatun #Yana daga cikin falalar salati Daren juma’a da yinin juma’a, Manzon Allah (SAW) yayi umarnin mu yawaita yi masa salati a wannan lokuta, saboda Hadisin Anas bin Malik (RA) yana cewa: Manzon Allah ( SAW ) ya ce: (Ku yawaita yi mini Salati a ranar juma’a da daren Juma’a, duk wanda ya yi min salati guda daya, Allah zai yi masa salati guda goma) Wasu Daga Cikin Falalar Yiwa Manzon Allah (SAW) Salati: Wanda yayiwa Manzon Allah (SAW) salati guda daya Allah zayyi masa salati guda goma Mafi kusanci da cancanta ga Manzon Allah (SAW) a ranar alqiyama, sune masu yawaita yiwa Manzon Allah (SAW) Salati #Kuma Manzon ALLAH (SAW) yana cewa, ” ku yawaita yi min salati, domin Allah Ya wakilta wani Mala’ika na musamman a wajan Qabarina, babu wanda zai yi min salati face wannan mala’ikan ya ce dani, wane dan wane ya yi maka salati yanzu Manzon Allah (SAW) wani mai zuwa ya zo min daga wajan Ubangijina,sai ya ce; ” Duk wanda ya yi maka salati guda daya daga cikin al’ummarka, Allah zai rubuta masa kyakkyawan aiki guda goma, Kuma a kankare masa laifuka guda goma, kuma a daukaka Darajarsa sau goma, kuma a maida masa salatin shima a yi masa Babu wanda zaiyiwa Manzon Allah ﷺ Sallama ,face Allah ya mayarmin da ruhina har sai na mayar masa da sallama KU biyomu a Kashi Na Biyu Domin karajin Wasu falaloli Daga MANZON ALLAH ﷺ