MUS'AB BN UMAIR . Ya taso a cikin jin dadi, gashi dan gata kuma kyakkyawa mai iya ado, dukkan wani taro baya cika idan babu Mus'ab a cikinsa. . Yana cikin wannan hali ne ya sami labarin kiran musulunci ta bakin amintacce Muhammadu[SAW],bai yi jinkiri ba wajen amsa kiran duk da sanin irin matsin da zai fuskanta. Mus'ab ya hakura da dukkan jin dadin duniya, ya maye shi da dandanar kuda da azabtarwa daga mutanensa. . Wata rana mus'ab ya taho gurin Annabi [SAW] sahabbai sun kewaye shi, lokacin da suka hango Mus'ab sukaga irin halin da ya shiga na kunci da takura sai suka sunkuyar da kawunan su suna kuka saboda tausaya masa. . A ranar yakin Badar shine yake rike da tutar Annabi [SAW] babbar ta Muhajirun hakama a yakin Uhudu inda a ranar yai shahada. . An ruwaito Annabi [SAW] ya tsaya a gaban Mus'ab da sauran wanda sukai shahada a Uhudu yana cewa: . "Lallai zanyi muku shaida cewa ku shahidai ne a gurin Allah ranar Alkiyama". . Ya Allah ka kara yarda da amincinka a garesu Alhamdulillah idan kunji gyara yan'uwa Ku gyara shine cikar 'yan'uwa idan kaga gyara kagyara saboda asamu mas,ala Allah kahada kawunan al'ummar Annabi sAww
MUS AB BIN UMAIR
Post a Comment
Post a Comment