HANYAR SHIGA ALJANNA CIKIN SAUKI 2
Cigaban bayaninmu nadazu
Godiya ta tabbata ga Wanda Ya zabi zababben Annabi a matsayin mafi zabin Ubangiji na hakika, kuma Ya yi ni’ima a gare shi da kyawawan halaye, Ya sanya shi halittarSa na farko gabanin halittar Annabi Adam kuma gabanin halittar sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu da abin da yake cikinsu. Tsira da aminicin Allah su tabbata a gare shi da alayensa zababbu da sahabbansa masu da’a da masu bin su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako ranar da mutane suke shiga Aljanna saboda yi wa Annabi (SAW) salati.
Idan kana son ka san hakikanin hakkin Manzon Allah (SAW) to ka dubi abin da Allah Madaukaki Ya ce game da hakkin Manzon Allah (SAW): “Ka ce idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni, sai Allah Ya so ku.” Babu makawa a yi bayanin wannan kalma dalla-dalla. Hakikanin sanin Annabi shi ne: Idan kuna son ku kasance ababen so ga Allah na gaskiya, to ku so ni, ku bi ni, sai Allah Ya so ku, saboda son da kuke mini.
Don haka hakikanin salati ga Annabi zababbe (SAW), ita ce hakikanin bin Manzon Allah cikin imani da kyautatawa. Allah Madaukaki Ya ce: “Hakika abin koyi mai kyau ya kasance gare ku game da Manzon Allah, ga wanda yake nufin Allah da Ranar Lahira, kuma ya ambaci Allah da yawa.” Yana daga cikin hakikanin yi wa Annabi (SAW) salati ka yi koyi da Manzon Allah a cikin komai. “Abin da Manzon (Allah) ya zo muku da shi ku yi rike shi, kuma abin da ya hane ku, to ku hanu.”
Manzon Allah mai girma ya ce: “Ku yawaita salati gare ni, domin abin da za a fara tambayarku a kabari a kaina ne.” Kuma ya sake cewa: “Ku yi salati a gare ni, domin salatinku a gare ni, zakka ce (tana tsarkake ku) kuma ita ana ninka ladanta ninkin ba ninki.”
Wadansu mutane sukan ce: Lallai Manzon Allah ya umarce mu da yin salati a gare shi, kuma ita ce Salatin Ibrahimiyya kawai, ba Salatin Ibrahimiyya ba ce kadai. Ku zo mu duba tare da ku abin da Shugaban Halitta masoyin Allah ya ce. Ya fadi cikin salati gare shi cewa: “Wanda ya ce: “Allahumma salli ala ruhi Muhammadin fil arwahi wa ala jasadihi fil ajsadi wa ala kabarihi fil kuburi.” Zai gan ni a cikin barcinsa, wanda ya gan ni a cikin barcinsa ya gan ni a Ranar kiyama, wanda ya gan ni Ranar kiyama zan cece shi, wanda kuma na cece shi, zai sha daga tafkina kuma Allah zai haramta jikinsa ga wuta!”
Wata rana Manzon Allah (SAW) ya fada wa sahabbansa game da salatin da Jibrila (AS) yake masa gaskatawa ga fadin Allah Madaukaki: “Lallai Allah da mala’ikunSa suna salati ga Annabi…” ya ce “Jibrilu ne ya jinkirtar da ni yana yi min salati, salatin da babu wani da ya taba yi min gabaninsa.” Sai Abubakar (RA) ya ce: “Yaya salatin da yake yi maka take ya Manzon Allah?” Sai ya ce: “Yana cewa: “Allahmma salli ala Muhammadin fi awwalina wal akhirina wa fil mala’ul a’ala ila yaumind din.”
Manzon Allah (SAW) ya kasance yana cewa: “Idan mutane suka zauna suna yi min salati, sai mala’iku su yi musu laima tu daga duddugensu har zuwa sararin samaniya da hannunwansu da takardun azurfa da alkaluman zinare suna taskance salati a kan Annabi (SAW) suna cewa ku kara, Allah Ya kara muku idan suka budada Ambato sai a bude musu kofofin sama kuma a amsa musu addu’a, kuma Ubangiji Ya fuskance su da fuskarSa matukar ba su shiga wata Magana sabaninsa ba.”
Yana daga cikin mafi soyuwan mutane ya kasance mai biyayya gare shi, kuma son Annabi wajibi ne a kan kowane Musulmi mai tauhidi. Kuma yana daga cikin son sa (SAW) yi masa salati da yi masa hakikanin biyayya.
“Kana son Allah amma kake bayyana sabonSa?
Wannan batu in aka duba bako ne.
Da sonka na gaskiya ne za ka bi Shi, Domin mai so, mai biyayya ga masoyinsa ne.”
“Lallai Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da ba ma’abucin zumunci hakkinsa. Kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da zalunci (tawaye). Yana yi muku wa’azi tsammaninku kuna tunawa.”
Allahumma salli ala mishkati jismihi. Allahumma salli ala zujajati aklihi. Allahmumma salli ala kaukabi sirrihi. Allahumma salli ala misbahi kalbihi…
Post a Comment
Post a Comment