Asslm alaikum warahmatullahi ta'a wabarakatuhu Ya Ubangiji! Ka kara salatinKa mai girma a kan AnnabinKa mafi girma da aminci, amincin da yake ciruwa kowace rana zuwa magaryar tukewa, kuma da alayensa da sahabbansa da wanda ya bi hanyarsa har zuwa ranar da Mahaliccinsa zai ce da shi: “Ka nemi ceto a ba ka ceto.” Bayan haka, ya ku bayin Allah! A hudubarmu ta yau za mu dubi falalar salati ga Annabi Mustapha (SAW) ne. Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi, Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi kuma ku yi sallama domin amintarwa gare shi.” Ya bayin Allah! Allah Madaukaki Ya umarce mu da sallolin farillai da azumin Ramadan da Zakka da Hajji da kyawawan ayyuka, kuma ba wanda Allah Yake yi daga cikin wadannan ayyuka, sai dai Ya yi mana bayani a cikin wannan aya cewa Shi ma Yana yin salati tare da Mala’ikunSa a kan masoyinSa Mustapha (SAW). An karbo daga Abdullahi bn Amru bn Al-As (RA) cewa lallai ya ji Manzon Allah (SAW) yana cewa: “Wanda ya yi min salati daya, Allah zai yi masa salati goma a madadinta. Kuma wanda Ya yi min salati goma Allah zai yi masa salati dari a madadinta. Wanda kuma ya yi min salati dari, Allah zai yi masa salati dubu a madadinta. Wanda kuma ya yi min salati dubu za mu yi kafada-da-kafada da shi wajen shiga Aljanna.” Kuma an karbo daga Ibn Mas’ud (RA) ya ce: “Lallai Manzon Allah (SAW) ya ce: “Mafi dacewar mutane a Ranar kiyama wanda ya fi su yin salati a gare ni.” Kuma an karbo daga Aus bn Aus (RA) ya ce: “Manzon (SAW) ya ce: “Lallai daga cikin mafiya falalar ranakun ranar Juma’a ce, don haka ku yawaita salati a gare ni a cikinta. Domin salatinku gare ana bijiro min da ita. Suka ce ya Manzon Allah ta yaya ake bijiro da salatinmu gare ka a bayan ka dudduge? Sai ya ce: “Allah Ya haramta wa kasa cin jikkunan annabawa.” Abu Dawuda ya ruwaito da isnadi mai inganci. Harkokin sallah tana da yawa bisa nau’o’inta da muhallinta sai an yi ta bisa kamanninta da kaifiyarta da sharuddanta. Amma salati ga Annabi (SAW) ta kubuta daga wadannan halaye gaba daya. Ana iya salati ga Annabi a kowane wuri ba tare da cutarwa ba, ba tare da niyya ko sharadi daga cikin sharuddan wata ibada ba. Kuma sabanin sauran ibadoji da in Allah Ya so Ya yarda da sashinsu kuma in Ya so Ya ki karba, ita salati ga Annabi Allah Ya yarda da ita daga kowane bawa nagari ko fasiki yanke. Wani ya rera cewa: “Ayyukanmu suna tsakanin karba da mayarwa, In ban da yin salati ga Annabi Muhammadu.” Kuma an karbo daga Aliyu (RA) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Marowaci shi ne wanda aka ambace ni bai yi min salati ba.” Tirmizi ya ruwaito shi kuma ya ce, Hadisi mai kyau mai inganci. Allahumma salli ala sayyidina Muhamad wa ala ali Muhammad kama sallaita ala Ibrahim wa ala ali Ibrahim fil alamina innaka hamidun majid. Allah ka lamincemana