Sayyida Ummi Ma'abidin(RTA). Tace: Manzon Allah Saww Mai Mabayyanin HASKENE Mai HASKEN FUSKA Ne. Mai KYAN Halitta ne. Bashi Da Girman Ciki Kuma Baza'a Suffantashi Da Mai Karamin Kai Ba (Wato Shi Ba Mai Karamin Kai Bane) Mutumne Mai Kyau. Kyakkyawa Sosai Kwayar Bakin Idonsa Baka ce Sidik Gashin Idonsa Da Na Girarsa Zara-zara ne Mai Matukar Dadin Sauti ne Mai Kyakkyawan Wuya Ne Mai Farin Kwayar Idanu Fari Fat Mai Kwalli Na Kaye Mai Kyakkyawan Madaukakin Karan Hanci, Mai Tsananin Bakin Gashi ne Idan Yayi Shiru Sai Nutsuwa Takara Daukaka A Gareshi Idan Kuma Yana Magana Sai Kwarjini Ya Kara Bayyana Da Daukaka A Tare Da Shi Shine Mafi Kyawun Mutane Mafi Kwarjininsu Daga Nesa Mafi Kyau. Mafi Haske Daga Kusa Mai Dadin Furici Mai Zance Dalla Dallah Filla Fillah Ba Siriri. Kai Kace Zancensa Tsararran Kayan Ado Ne A Tsare Das'das Mai Madai daicin Tsayi Ne Ido Baya Munanashi don Gajarta Kuma Ba Zai Munanashi Ba Dan Tsayi Shi Kyakkyawan Reshe Ne A Tsakanin Rassa(2) (Wato Shi Bagare Bane Chan. Kuma Ba dogo Ba ne Can) Shi ne Mafi Kyawu A Hasken Abubuwan Duba Guda(3) Shine Mafi Kyawun Girman Alkadari Yana Da Abokai Suna Kewaye Da Shi. Idan Yafada Sai Suyi Kawai Su Saurari Maganarsa Idan Yayi Umarni Sai Nan Da Nan Suyi Gaggawar Cika Umarninsa (Abokansa)Suna Mutukar Girmamashi Kuma Suna Mutukar Gaggauta Cika Umar Ninsa Shine Wanda Mutane Suke Dandazo Zuwa Gareshi Ba Mai Daure Fuska Bane(ma'ana Baya Daure Fuska Yana Sakin Fuska Ga Kowa) Shi. Manzon Allah Saww Ba Abin Zargi Bane (Imam Hakim Ya Fitar Dashi. Kuma Hadisine Mai Kyau. Ingantacce Imam Hussaini Ya Ruwaitoshi* Allahu Akbar wllh ruhi baya gajiya dajin zancen abin kaunarta