LABARIN WANI MAI ZAGIN SAHABBAI ×=============================× Khalaf bn Tameem ya bamu labari cewa yaji Abul-Haseeb yana cewa: "Na kasance ni mutum ne Attajiri mai yalwar Dukiya sosai. Kuma na kasqnce ina zaune acikin MADA'INU KISRA (wato babban birnin Qasar Sham, ko kuma Iran ta yanzu, Inda sarkin Kisra ya zauna). Wata rana ina zaune sai wani yarona yazo ya bani labarin cewa "GA WANI MUTUM CHAN YA MUTU ARUMFAR KASUWA, AMMA AN RASA LIKKAFANIN DA ZA'A RUFESHI DASHI". Sai na tashi na taho kasuwar, na shiga rumfar inda na tarar da Mamacin akwance, an dora wani tubali (brick) abisa ruwan cikinsa. Abokansa da na tarar tare dashi suna zazzaune, su suka ambata min irin yadda wannan mamacin yake da Kwazo wajen ibada, suka gaya min falalarsa da darajojinsa sosai. Daga jin wannan, sai na tura asiyo Masa likkafani, Sannan na biya wani mai tonon Qabari yaje ya tona masa, Sannan kuma ni da kaina na girka ruwa domin muyi masa wanka. Muna cikin haka kenan sai muka ga Mamacin nan ya tashi ZUMBUR ya zauna!! Yana Eehu!! Yana Kururuwa!! "WAYYO NI KAINA!!! WUTA!!! WUTA!!! NA HALLAKA!!!. Sai abokansa duk suka fice aguje!! Ni kuwa sai na matsa kusa dashi, na rike kirjinsa, na girgizashi sannan nace masa: "KAI WANENE? KUMA WANNE HALI KAKE CIKI? " Sai yace mun: "Nayi abokantaka ne da Maluman Koufah, Sai suka shigar dani cikin ra'ayinsu na ZAGIN SAYYIDUNA ABUBAKAR DA UMAR DA KUMA YIN BARAA'A DAGA GARESU!" Sai nace masa "YI ISTIGHFARI, AMMA KAR KA KOMA (CIKIN RA'AYINSU)". Sai ya amsa min da cewa "Ai wannan duk ba zai amfaneni ba! Tunda gashi yanzu har an riga an tafi dani wajen zamana acikin Wuta, kuma ance mun: "Da sannu zaka koma cikin abokanka, don ka basu labarin dukkan abubuwan da ka gani (na azaba) Sannan zaka dawo izuwa yanayinka da kake ciki". Bai gama rufe bakinsa daga wannan maganar ba, sai muka ga ya koma ya zube kamar yadda da yake Matacce.. Sai na zauna na jira har wanda na aikasu sayowa likkafanin nan suka dawo, na karbe likkafani na, Sannan na mike tsaye nace "WALLAHI BA ZAN YI MASA LIKKAFANI BA, KUMA WALLAHI BA ZANYI MASA WANKA BA, KUMA BA ZAN SALLACESHI BA!!! " Sai nq fita na tafi na barsu anan. Amma daga baya na samu labarin cewa abokansa da suke tare dashi, dama ra'ayinsu guda dashi. Don haka su sukayi masa wanka suka sallaceshi. sannan suka juyo suna cewa mutanen da suke wajen: "Wannan abinda kuka gani ya faru akan wannan mamacin namu, bq komai bane illa shaitanu ne suka magana ta bakinsa". – Ni kuwa nace Kaji masu taurin kai fa!! – anyi muku gargadi Qarara amma baku Wa'aztu dashi ba! Khalaf yace na tambayi ABUL HASEEB cewa Wannan abinda ka gaya mun, shin ka shaidar da faruwarsa? Sai yace mun "WALLAHI NA GANI DA IDONA, KUMA NAJI DA KUNNENA! ". Sai nace tunda hakane, ni kuwa zan isar dashi ga mutane. * Babban Malamin hadisin nan mai suna IBNU ABID DUNYA shine ya kawo wannan labarin acikin littafinsa mai suna "MAN 'AASHA BA'ADAL MAWTI" akan shafi na 17. * MUKHTASARU TAREEKHI DAMASHQA - wanda Ibnul Manzour ya rairayo daga ainihin Babban Littafin na Ibnu Asakira, juzu'i na 6 shafi na 47. Fatan ZAUREN FIQHU shine Allah yasa wannan ya zama izina ga masu irin wannan halayyar aduk inda suke.