Takaitaccen tarihin Imam Asshafi'ee
TAKAI TACCEN TARIHIN
IMAM MUHAMMAD ASH-SHAFI'E
*Imam Ash-shafi’e asalin sunansa shi
ne: Muhammad Bin Idris Bin Abbas Bin
Usman Bin Shafi’e; Abu Abdullah, Ash-
shafi’e, Al-qurashi, Al-makki, nasabarsa tana tukewa zuwa ga Lu’ayyu Bin Galib,
wato kakannin Manzon Allah(Sallallahu
Alaihi Wa Sallam ). An haifi Imam Ash-
shafi’e a shekarata (150A.H) a garin
Makkah, mahaifinsa ya rasu tun yana
yaro karami, don haka ya taso ka...rkashin kulawar mahaifiyarsa ne.
Imam Shaffi'e ya fara neman ilimi tun
yana yaro, ya fara da karatun harshen
larabci da kuma wake-waken larabawa
har ya tumbatsa a cikin wannan fanni,
sannan ya fuskanci karatun fiqihu har ya zamanto jagora a zamaninsa. Imam
Ash-shafi’e ya karanta littafin Muwadda
a wajen Imam Malik, ya kuma yi
wallafe-wallafe na littattafai da dama,
daga cikin mafi shaharar littattafansa
akwai: Ar-Risala, da Al-Um, da Al- Musnad, da kuma As-Sunan. Imam Ash-
shafi’e yana cewa: neman ilimi ya fi
sallar nifila, duk wanda ya koyi qur’ani
matsayinsa zai daukaka, duk wanda ya
karanta hadisi hujjarsa zata yi karfi, duk
wanda bai kame kansa ba daga sabon Allah to iliminsa bai
masa amfani ba. Imam Ash-shafi’e ya
rasu a shekarata (204A.H).
Allahu akbar kaji manyan bayin Allah
Post a Comment
Post a Comment